Har yanzu Hashimu Dungurawa ne halastaccen shugaban NNPP na Kano – Shugabancin jam’iyyar na ƙasa
Har yanzu Hashimu Dungurawa ne halastaccen shugaban NNPP na Kano – Shugabancin jam’iyyar na ƙasa

Har yanzu Hashimu Dungurawa ne halastaccen shugaban NNPP na Kano – Shugabancin jam’iyyar na ƙasa
Shugabancin Jam’iyyar NNPP ya ƙi amincewa da dakatar da Hashimu Dungurawa, shugaban jam’iyyar na jihar Kano.
A ranar Litinin, wasu mambobin zartarwa na jam’iyyar a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, mazabar Gargari, suka dakatar Dungurawa daga mukaminsa saboda zargin raba kan jam’iyyar da tada tarzoma a ciki.
Dungurawa wanda na hannun daman Sanata Rabiu Kwankwaso ne, tsohon gwamnan Kano kuma Jagoran NNPP na ƙasa.
A ranar Talata, kwamitin zartarwa na jam’iyyar a Kano ya nada Abdullahi Abiya a matsayin shugaban NNPP na rikon kwarya a jihar.
A cikin wata sanarwa, Ladipo Johnson, mai magana da yawun NNPP, ya ƙi amincewa da dakatar da Dungurawa, inda ya bayyana matakin a matsayin “ba daidai ba, ba na dimokiradiyya ba, babu inganci, babu tasiri kuma ba shi da wata ma’ana.”
“Abin da suka yi hakika ya zama babban aikin adawa da jam’iyya domin ya keta tanade-tanaden da ke cikin tsarin jam’iyyar,” in ji sanarwar.
Johnson ya ce Dungurawa “shugaba ne mai gaskiya, mai aiki tukuru, kuma mai kishin aiki wanda shugabancinsa da aikinsa a tsawon lokaci sun kasance abin koyi kuma sun taimaka wajen ci gaban jam’iyyar a Kano.”
