Politics

Wata dama ce na samu ta buɗe sabon babi na rayuwa, musamman a fagen siyasa.

Tsohon ɗan majalisar wakilai da shugaba Tinubu ya yi wa afuwa a kan laifin rashawa da kotu ta kama shi da shi, Faruk Lawan ya ce an ba shi wata dama ta buɗe sabon babi na rayuwa, musamman a fagen siyasa.

Tsohon ɗan majalisar wakilai da shugaba Tinubu ya yi wa afuwa a kan laifin rashawa da kotu ta kama shi da shi, Faruk Lawan ya ce an ba shi wata dama ta buɗe sabon babi na rayuwa, musamman a fagen siyasa.

Farouk Lawan na cikin mutane 175 da shugaban Najeriya ya yi wa afuwa a ranar Alhamis, 9 ga watan Oktoban 2025, bayan amincewar majalisar magabata.

Tsohon ɗan majalisar wanda ya wakilci mazaɓar Bagwai/Shanono ta jihar Kano a majalisar wakilan Najeriya ya tsinci kansa a badaƙalar cin hanci da rashawa a 2012, inda aka zarge shi da karɓar cin hanci domin cire sunan wani kamfani daga jerin kamfanonin da ke almundahana da kuɗin tallafin mai a Najeriya.

A ranar 22 ga watan Yunin 2021 wata babbar kotun tarayya ta yanke wa Faruk Lawan hukuncin ɗaurin shekara bakwai a gidan yari bayan kama shi da aikata laifuka uku da hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC ta zarge shi da aikatawa.

Ya ɗaukaka ƙara har zuwa kotun ƙoli, kuma duk da cewa kotun ɗaukaka ƙara ta wanke shi daga biyu daga cikin laifukan da ake zarginsa da aikatawa, Lawan ya yi zaman yari, kuma ya kammala acikin watan Oktoban 2024.

Faruk Lawal ya ce bayan fitowarsa daga gidan yari a 2024, ya ɗauki matakai na sauya tsarin tafiyarsa a siyasa inda ya raba gari da tafiyar Kwankwasiyya da aka san shi da ita tun asali.

 

Ya ce ko a lokacin da ya shiga gidan yari yana matsayin ɗan jam’iyyar PDP ne, amma daga baya da aka zo zaɓen 2023, ya umarci duk mutanen shi su shiga tafiyar NNPP, kuma hakan suka yi.

Ya ƙara da cewa ”duk lokacin da Allah ya sa ka shiga jarrabawa, to Allah yana haska maka ka san su waye abokan tafiyar ka, su waye ba abokan tafiyar ka ba.

”Idan kana irin wannan wajen (gidan yari) kana da dogon lokaci da za ka yi nazari a kan mu’amular ka.”

Ya yi bayanin cewa tun daga lokacin zaman sa a gidan yari har zuwa lokacin a ya fito akwai abubuwan da ya yi fatan za su canza, amma abin ya gagara.

Tsohon ɗan majaisar ya yi zargin cewa duk da kusancinsa da tafiyar kwankwasiyya, akwai wani jigo a tafiyar da bai taɓa kira ba, ko dai ya yi mashi jaje ko kuma murnar fita daga gidan yari

”Yau shekara ta guda, ko waya bai yi ya ce yana mani fatan alheri ba, na cewa Allah ya fito dani daga wannan waje, yana yi mini addu’ar.”

Ya kuma bayyana cewa duk da yake a yanzu baya da ra’ayin tafiyar kwankwasiyya, amma har yanzu suna mutumci tsakanin shi da jagoran tafiyar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Farouk Lawan ya ce a halin da ake cikin yanzu ya mayar da hankali ne ga jam’iyyar da ta karɓu a ƙasa baki ɗaya, don haka ”ya kamata a ce siyasar mutum ta faɗaɗa, kuma jam’iyyar da aka koma ta NNPP, ni ina ganin wannan kuttun ya yi mani ƙanƙanta.

 

”Idan mutum ya shiga jarrabawa kuma Allah ya kawo wata dama ta afuwa, to dole a yi farin ciki. Gaskiya da ni da iyalina da dukkan masoyana a duk inda suke, na san ranar da aka yi wannan, ranar farin ciki ce gare mu baki ɗaya,”

Ya ƙara da cewa ”Kuma rana ce da muka yi amfani da ita wajen godiya ga Allah domin shi ne ya yi mana, sannan da godiya ga shugaban Najeriya Bola Tinubu saboda ya yi abin da ya kamata dole a yaba mashi.”

Tsohon ɗan majalisar ya yi waiwaye a kan yadda rayuwa ta kasance a lokacin da yake zaman yari, inda ya ce dama can ya riga ya sallama komai ga Allah, don haka yana sane cewa ɗan Adam ba ya wuce ƙaddarar shi, lamarin da ya ce ya ƙarfafa masa gwiwa sosai.

”Wannan ya sa tun kafin na bar koto hankali na a kwance yake, kuma na gamsu da cewa wurin nan da zan je mutane zan samu, sannan indai har za su iya rayuwa a wajen, to ni ban ga dalilin da ya sa ni ba zan iya rayuwa a wajen ba,”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button