Uncategorized

Sama Da Ƙungiyoyi 50 A Jihar Kano Sun Yi Kira Ga Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf Da Ya Maida Alhaji Namadi Kan Kujerarsa Ta Kwamishinan Sufuri Domin Ya Ci Gaba Da Aikin Taimakon Al’umma Da Yake Yi

Sama Da Ƙungiyoyi 50 A Jihar Kano Sun Yi Kira Ga Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf Da Ya Maida Alhaji Namadi Kan Kujerarsa Ta Kwamishinan Sufuri Domin Ya Ci Gaba Da Aikin Taimakon Al'umma Da Yake Yi

A cewar ƙungiyoyin, kwamishinan sufuri Alhaji Ibrahim Namadi da gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sauke bisa zargin sanya hannu a belin wani dilan miyagun ƙwayoyi Suleman Ɗanwawu, kwamishina ne jajirtacce mai ƙoƙarin taimakon al’umma wanda a yau mutane da dama da yake taimkawa suna cikin mawuyacin hali saboda wanda yake taimaka musun babu dama a hannunsa.

 

Cikin sanarwar da ya fitar a madain ƙungiyoyin, Suleman Ahmad Ibrahim Gwammaja, ya bayyana cewa, “Muna kira ga mai girma gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba K. Yusuf da ya taimaka ya maida Alhaji Namadi kujerarsa ta kwamishinan sufuri domin ya ci gaba da aikinsa na hidimtawa Kano da taimakon al’umma. Akwai ɗumbin mutane waɗanda da shi suka dogara gaba ɗaya yanzu da dama suna cikin tsananin damuwa”. Ya ce.

 

Ya ƙara da cewa, “Sannan muna fatan mai girma gwamna zai yi duba da cewa kwamishina Namadi tuni ya cire hannunsa a belin kuma wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyin yana zuwa kotu ana ci gaba da yi masa shari’a. Muna fatan mai girma gwamna zai saurari buƙatarmu ya maida shi kan kujerarsa ya ci gaba da taimakon al’umma”. In ji shi.

Me zaku ce?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button