SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR KABO YA KARA GWANGWAJE YAN GWAGWARMAWA DA SABBIN MOTOCI
SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR KABO YA KARA GWANGWAJE YAN GWAGWARMAWA DA SABBIN MOTOCI

SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR KABO YA KARA GWANGWAJE YAN GWAGWARMAWA DA SABBIN MOTOCI
Shugaban Karamar Hukumar Kabo, Comrade Lawan Najume Kabo, ya kara nuna kishin sa ga ƴan gwagwarmayar yankin ta hanyar rarraba sabbin motoci ga mutum bakwai (7) daga cikin jagororin gwagwarmaya a karamar hukumar.
Wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen gwamnati na karfafa gwiwar matasa da masu fafutuka wajen gudanar da ayyukan cigaba da inganta rayuwar al’umma.
A yayin bada tallafin, Shugaban ya bayyana cewa wannan baiwa tana nuni da muhimmancin haɗin kai da sadaukarwa wajen tabbatar da nasarar manufofin gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Ya kuma shawarci waɗanda suka amfana da su yi kyakkyawan amfani da motocin domin ci gaban al’umma, ba don son zuciya ba.
A nata bangaren, waɗanda suka karɓi motocin sun nuna farin ciki da godiya ga shugaban bisa irin wannan kulawa da kyautatawa da yake nunawa ga masu gwagwarmaya da mutanen Kabo gaba ɗaya.
