Politics

GWAGWARMAYAR SIYASAR YANCHI DA SANIN YANCHIN KAI ITA MUKA SAKA A GABA

GWAGWARMAYAR SIYASAR YANCHI DA SANIN YANCHIN KAI ITA MUKA SAKA A GABA

GWAGWARMAYAR SIYASAR YANCHI DA SANIN YANCHIN KAI ITA MUKA SAKA A GABA

Tun farkon lokacin da muka tsinci kanmu cikin gwagwarmayar siyasa — wacce muka gada daga magabatanmu da iyayenmu irin su Alhaji Salisu Mu’azu Shugaba Kiru — muka dauki nauyin fadi-tashin al’amuran al’umma da gaskiya da aminci.

Abin da muka gada a siyasa shi ne sani da kare yancin kai, da riko da amanar jam’iyya da dan takara da muke mara masa baya. Muna yin wannan ne ba don kwadayin abin duniya ba, sai dai don cika alkawari da gaskiya. Tsoro ko ja da baya ba takenmu bane, idan aka duba irin jagororin da muka taba yi wa aiki a baya, da kuma wadanda muke tare da su yanzu.

Mu kalli Sen. S A Kawu Sumaila, OFR Ph.D , Sanatan Kano ta Kudu — babu irin gwagwarmayar da bamuyi ba wajen tallata takararsa: ruwa, rana, da iska basu hanamu aikinmu ba. Duk da haka, bamu taba neman abin duniya daga gare shi ba, muka tsaya da shi da gaskiya da amana.

Haka kuma, a wajen Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, mun ba shi gudunmawa ta gaskiya, wacce har shi kansa ya yi mamakin yadda muke samun kudin gudanar da ayyuka, saboda ba da kudinsa muke yi ba.

Yanzu kuma, mu dubi Mai Girma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na Najeriya, DSP Sanata Barau I. Jibrin (Maliya). Tun daga farko muka tsaya da shi da amana, kuma shi kansa ya sani cewa ko sisinsa bai taba bamu ba, kuma bamu taba nema ba. A yau, da kungiyar Northwest Youth Advancement Network (NYAN) da muka kafa, da guminmu muke tafiyar da komai — ba tare da sisin kowa ba. Allah Shaidane, kuma shi DSP kansa shaidane, haka suma duk al’ummar da muke NYAN dasu suma shaidane, daga karshe inason tabbatarwa da masu rubutu samun shugabanci irin na SA Contact and Mobilization na DG Ahmad Tijjani Salisu Kiru zaiyi wahala duba da yadda yake gudanar da shugabancinsa cikin gaskiya da rikon Amana da dukiyarsa da lokacinsa.

Haka nan, mu kalli dan Majalisar Jihar mu, Hon. Usman Abubakar Rabula, wanda shima tun daga lokacin takararsa har zuwa zabe, mun ba shi gudunmawa daidai gwargwadonmu.

Alhamdulillah, akidarmu da takenmu ya tabbata:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button