Uncategorized

Kwamishinan Yada Labarai da Al’amuran Cikin Gida na Kano Ya Zauna da Matasan da Suka Mika Wuya

Kwamishinan Yada Labarai da Al’amuran Cikin Gida na Kano Ya Zauna da Matasan da Suka Mika Wuya

Kwamishinan Yada Labarai da Al’amuran Cikin Gida na Kano Ya Zauna da Matasan da Suka Mika Wuya

Kwamishinan Yada Labarai da Al’amuran Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jagoranci zaman kwamitin Save Corridor karo na uku tare da matasan da suka mika wuya, domin ci gaba da tantance su da kuma tattauna hanyoyin cika musu alkawuran da gwamnatin jihar ta dauka a kansu, muddin suka tuba suka ajiye makamai.

Taron, wanda aka gudanar a dakin taro na Babale Suite a yau, ya samu halartar manyan baki da suka hada da iyayen kasa, wakilan masarautu, da shugabannin kungiyoyin sa-kai.

A yayin zaman, Comrade Waiya ya jaddada kudirin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da tallafawa shirin Save Corridor, wanda ke da nufin tabbatar da zaman lafiya, farfado da rayuwar matasa, da kuma mayar da su cikin al’umma ta gari.

Ya kuma yaba da irin jajircewar kwamitin da sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da nasarar shirin, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da bayar da goyon baya domin ganin an cimma burin da aka sa gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button