Dakarun Sojojin Najeriya sunyi Nasara a shanono dake jahar kano
Dakarun Sojojin Najeriya sunyi Nasara a Shanono Dake jahar kano
Gamayyar dakarun tsaro karkashin rundunar Operation MESA da aka kai karamar hukumar Shanono a jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya ta kawar da ‘yanbindiga 19 daga doran duniya bayan wata taho mu gama da suka yi a wani yanki na karamar hukumar ta Shanono da aka samu bullar ‘yanbindiga
Wannan na kunshe ne a sakon mataimakin daraktan yada labaran rundunar sojan Najeriya
Kaftin Zubairu yace sojojinsu biyu da wani Dan bijilanti sun rasa rayuwarsu a yayin batakashin da suka yi da ‘yanta’addar.
“ Operation MESA a karamar hukumar Shanono ta dakile yunkurin ‘yanta’addar tare da ba da kariya ga al’umma a karamar hukumar ta Shanono.”
Rundunar sojan Najeriya dai ta bukaci al’umma a yankin su zama masu sa idanu tare da ba da duk wani rahoton motsi da basu gamsu da shi a yayin da sojan na Najeriya suka mayar da hankali wajen ba da kariya ga rayuka da dukiyoyin al’umma.
