Uncategorized

Abdullahi Girma Gwale ya nuna damuwarsa akan masu futa daga NNPP kuma “yan gwagwarmaya har 30 wannan abin ta kaici ne a gare mu

Abdullahi Girma Gwale ya nuna damuwarsa akan masu futa daga NNPP kuma "yan gwagwarmaya har 30 wannan abin ta kaici ne a gare mu

Abdullahi Girma Gwale ya nuna damuwarsa akan masu futa daga NNPP kuma “yan gwagwarmaya har 30 wannan abin ta kaici ne a gare mu.

 

Tsohon Dan Takarar Chairman a karamar hukumar Gwale a Jahar Kano Kuma Jigwan jam’iyyar NNPP, Hon Abdullahi Inuwa Girma Gwale ya nuna damuwarsa kan wasu ‘Yan Social media da’yan Kwankwasiyya Reporters a karamar hukumar Gwale sama da 30 da suka sauya sheƙa zuwa cikin APC Kano.

 

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook Abdullahi Girma Gwale ya ce masu sauya sheƙa da sukeyi a halin yanzu “yan gwagwarmaya ke yawan furtawa da kuma ayyana rashin kulawa da mutunta su da jahosu a jiki babbar matsala ne a karamar hukumar Gwale da ma jahar

 

Abdullahi Girma Gwale yace dan Allah ayi hakuri a da kata a daina fucewa daga Jam’iyyar NNPP Muna sonku ‘yan gwagwarmayar za.a kawo gyara insha Allahu

 

Haka kuma, ya shawarci gwamnatin karamar hukumar Gwale da ta nada gwamata na musamman da kuma na dindindin domin su tattauna da’yan Kwankwasiyya Reporters da’yan Social media a karamar hukumar Gwale da kare muradun Kano a matakin Kwankwasiyya.

 

Abdullahi Girma Gwale ya kuma yi kira ga ‘Yan karamar hukumar Gwale da su haɗa kai wajen fuskantar matsin lamba daga waje da na cikin gida, yana mai jaddada muhimmancin karfafa hadin kai da zaman lafiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button