Uncategorized

BAJE KOLIN KASUWANCI NA BANA KASHI NA 46 ZAI ZAMA MAI ABIN MISALI

Cibiyar Kasuwanci Masana’antu, Ma’adinai da Noma ta Jihar Kano KACCIMA ta bayyana cewa baje kolin kasuwanci na ƙasa na bana da ke tafe zai zama na musamman a tarihin bajekolin da aka gudanar a jihar Kano a baya.

Shugaban cibiyar na jihar Kano Alh.Hassan Darma shine ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a shirye shiryen bajekolin da kana dake tafe. Sshugaban ya ce sama da kamfanoni dari bakwai daga ciki da ƙasashen waje kamar China, Turkiyya, Pakistan Ghana, Niger da sauran sune ake sa ran za su halarci bikin na bana.

Haka zalika ya ce Ministan Kasuwanci da Zuba Jari kasa zai halarci bikin, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, zai kaddamar da shi a hukumance, tare da Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, a matsayin babban mai masaukin baki.

Ana sa bangaren Alh.Kabir Muhammad Adam Wanda shine mataimakin shugaban cibiyar kuma shugaban riko na kwamitin shirya baje kolin na bana ya ce an samar da sabbin tsare tsare na cigaba kamar hasken wutar lantarki, tsaro , da kuma wuraren baje koli na zamani ga baki da yan gida a harabar filin baje kolin Kano.

Alh. Sabit Muhammad mukaddashin shugaban cibiyar na daya yace sun yi tsari mai kyau wurin tabbatar da cewa kudin shiga bajekolin na bada yayi sauki don bawa kowa damar zuwa don baje hajara shi.

An tsara gudanar da baje kolin na 46 daga ranar 27 ga Nuwamba zuwa 27 ga Disamba, 2025, a filin bajekolin na bana.

Ma’ajin cibiyar Alh. Umar Ladiyo ta bukaci ’yan kasuwa da jama’a gaba ɗaya da su yi amfani da wannan dama wurin tallata kasuwancin su, zuba jari, da bunƙasa kirkire-kirkire a Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button