News

Kungiyar Malaman Jami’a ASUU ta shiga yajin aiki gargadi na mako biyu

Ƙungiyar malaman jami’a ta kasar nan ASUU ta fara yajin aikin gargaɗi na makonni biyu bayan wa’adin da ta bai wa gwamnatin tarayya domin biyan buƙatun ta ya cika a ranar Lahadi.

Shugaban ƙungiyar, farfesa Chris Piwuna, ya shaidawa wani taron manema labarai a jami’ar Abuja a ranar Lahadi cewa shugabannin ASUU sun cimma matsayar shiga yajin aikin ne bayan wa’adin kwanaki 14 da ƙungiyar ta bai wa gwamnati daga ranar 28 ga watan Satumba ya cika, ba tare da gwamnatin ta yi abin da ya kamata ba.

Ya ce da wannan sanarwa “Muna umartar dukkan rassan ASUU su janye daga gudanar da duk wani aiki daga safiyar ranar Litinin 13 ga watan Oktoban 2025. Kuma yajin aikin gargaɗin zai shafi kowanne irin aiki da malaman jami’a ke yi, kamar yadda babban kwamitin ƙoli na shugabancin ƙungiyar ya amince.

Ƙungiyar malaman jami’ar ta zargi gwamnati da rashin mayar da hankali wajen aiwatar da yarjejeniyar da ke tsakanin su, da kuma rashin gaskiya a tattaunawa da suke yi domin kaucewa shiga yajin aikin.

Farfesa Abdulkadir Muhammad, jami’in tsare-tsare na ƙungiyar ASUU reshen jihar Kano ya shaidawa gwamnatin tarayya cewa ta ƙure duk wata damar yin sulhu da kaucewa shiga yajin aikin da ASUU ta ba ta a baya.

“Saboda da haka muka ga babu abin da ya dace mu yi illa mu bai wa mambobinmu umarni su janye daga aiki na sati miyu, da fatan cewa wannan mataki da muka dauka zai fargar da gwamnati ya sa ta yi abin da ya kamata,” In ji farfesa Muhammad.

Ya kuma bayyana cewa ƙungiyar tana sane da yadda matakin nata zai iya shafar karatun ɗaluban su, amma kuma ba su da wani zaɓi da ya zarce shi.

”Yayin da kazo ka zauna ka ce ka ɗauki ma’aikaci ya yi maka aiki….ba ka iya biyan sa haƙƙin sa, wannan ma zai iya sa ma’aikacn bai yi abin da ya akamata ba kuma zai shafi ɗaluban.

Ƙungiyar malaman jami’ar dai ta ce sabuwar dambarwa a tsakanin ta da gwamnatin tarayya ta samo asali ne daga halin ko in kula da gwamnatin ke nunawa a matakai daban-daban na tattaunawar neman mafita da suka yi a tsakanin su.

ASUU ta jajirce kan neman gwamnatin ta aiwatar da yarjejeniyar da ta ƙulla da ita a 2009, wadda ta yi tanadin yadda za a kula da walwalar malaman jami’ar, da kula da jami’oin ƙasar da kuma sauran batutuwan da suka shafi tafiyar da harkokin jami’a.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta mayar da martani ga ASUU, inda ta yi gargaɗin cewa za ta aiwatar da tsarin ‘ba aiki, babu biyan albashi’ kan malaman idan suka shiga yajin aikin.

Kakakin ma’aikatar ilimi ta Najeriya, Folasade Boriowo, ta ce gwamnati ta yi wa ƙungiyar tayi mai gwaɓi, kuma tana jiran martanin ta.

Ta ce daga cikin tayin da gwamnati ta yi wa ASUU har da matakan magance muhimman matsalolin da ƙungiyar ta gabatar da suka haɗa da inganta yanayin aiki da gyara a tsarin gudanar da jam’oi da kuma walwalar malaman.

Ta kuma zargi ASUU da rashin bayar da haɗin kai, duk da kokarin da ta ce gwamnati na yi domin kaucewa shiga yajin aikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button